Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya nakalto Faleh Fayyad shugaban rundunar yana fadar haka a safiyar yau Talata a birnin Bagdaza babban binrin kasar, ya kuma kara da cewa tare da shigowar Karin mutane 30,000 cikin rundunar, a yanzu tana da mayaka kimani 167, 000.
Har’ila yau shugaban rundunar ‘Asa’ib Ahlul-Hakkin Kais Huz-Ali yay i maraba da shigowar sabbin mayaka a cikin rundunar Hashadu, ya kuma gudewa ma’aikatar tsaron kasar da amincewa da ta yi na wannan Karin.
An kafa rundunar mayakan sa kai na Hashdu ne a shekara ta 2014 a lokacin mayakan ‘yan ta’adda ta Daesh suka mamaye wasu yankunan na kasar Iraki. Kuma rundunar ta kawo karshen samuwar kungiyar bayan shekaru 3 da fafatawa. A shekara ta 2017 majalisar dokokin kasar ta sanya rundunar cikin jami’an tsaron kasar ta Iraki.
A halin yanzu ma rundunar tana ci gaba da kakkabo ragowar mayakan na Daesh a cikin kasar.
342/